Home Ƙasashen waje Gidaje 43,000 ne a Burtaniya su ka shirya karɓar ƴan gudun hijirar Ukraine

Gidaje 43,000 ne a Burtaniya su ka shirya karɓar ƴan gudun hijirar Ukraine

0
Gidaje 43,000 ne a Burtaniya su ka shirya karɓar ƴan gudun hijirar Ukraine

 

Gidaje 43,000 ne su ka yi tayin tarbar ƴan gudun hijirar Ukrain a matsayin wani bangare na shirin tallafi na gwamnatin Birtaniyya, a cewar Sashen kula da Gidaje da Al’umma.

Kakakin Ma’aikatar a jiya Talata ya ce alkaluman sun yi daidai a yanzu amma za su iya ci gaba da karuwa.

Ya tabbatar da cewa wata kafar yanar gizo da aka buɗe mai suna ‘Homes for Ukraine’ da a ka kirkira na wucin-gadi “ya yaɗu a yammacin Litinin saboda karamcin da jama’ar Burtaniya su ka yi wajen ba da gudummawa ga wadanda ke tserewa rikici da Rasha.

Sakataren al’ummomin Michael Gove ya ba da cikakken bayani game da shirin daukar nauyin a zauren majalisar a ranar Litinin.

Ya kara da cewa shirin zai baiwa daidaikun mutane, kungiyoyin agaji, kungiyoyin al’umma da kuma ‘yan kasuwa su kai mutanen da su ke tserewa yakin Ukraine cikin kwanciyar hankali, ko da kuwa ba su da wata alaka da Burtaniya.

Ya ce, “Duk wanda ke da daki ko gida zai iya ba da shi ga wani mutum ko dangi dan Ukrainian, kodayake wadanda aka bayar za a tantance su kuma masu neman Ukraine za su yi gwajin tsaro.

“Mambobin jama’a da ke ba da masauki ga ‘yan Ukrain dole ne su yi hakan na akalla watanni shida.”

Ya kara da cewa, za a ba wa ‘yan Ukraine da suka dauki nauyin ba su izinin zama a Biritaniya na tsawon shekaru uku, tare da damar yin aiki da kuma samun damar yin hidimar jama’a.

A cewarsa, wadanda ke ba da wurin zama za su karɓi biyan haraji na zaɓi na kowane wata na Yuro 350 (dalar Amurka 455.80).