
Gidauniyar Aliko Dangote tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da gidauniyar Bill da Melinda Gates sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna kan rigakafin da ake yi Akai-akai, a jihar.
An fara sanya hannu kan yarjejeniyar ne a shekarar 2012, lokacin da gidauniyar Aliko Dangote da gwamnatin jihar Kano da gidauniyar Bill da Melinda Gates suka yanke shawarar yin aiki tare don inganta lafiyar mata da yara a Kano, jiha ta biyu mafi yawan al’umma a Nigeria.
Dangane da nasarorin da aka cimma a yarjejeniyar fahimtar juna ta farko, duk bangarorin uku sun rattaba hannu kan takardar a karo na biyu a shekarar 2017 a wani yunkuri na inganta manufar da aka cimma a baya.
Sai dai kuma, rattaba hannu kan yarjejeniyar lafiya karo na uku, a wannan karon, UNICEF ma sun shigo cikin yarjejeniyar.
Da take jawabi gabanin rattaba hannu kan yarjejeniyar a hukumance a ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar Kano, Manajan Darakta kuma Babban Jami’ar Gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Yousefou, ta taya gwamnatin jihar Kano murnar cimma muradun wannan taron karawa juna sani.
Zouera Yousefou ta yabawa gwamnatin jihar bisa kokarinta na ci gaba da samar da kudade ga dukkan ayyukan Rigakafi, ta yadda za a kara yawan kasafin kudin jihar da kashi 22 cikin dari a cikin shekaru 6 da suka gabata, duk da kalubalen da ake fuskanta a kasafin kudi.
“Muna buƙatar tabbatar da cewa mun yi amfani da darussan da muka koya daga shekarun da suka gabata, don haɓakawa da aiwatar da ingantattun dabarun da suka dace waɗanda za su sa mu ci gaba cikin hanzari kuma a ƙarshe mu cimma burin da yasa aka yiwa yarjejeniyar ta lafiya”. Inji ta
Shugabar Gidauniyar ta kuma bukaci sarakunan gargajiya da su jajirce wajen k tabbatar da cewa al’umma sun yi amfani da muhimman ayyukan kiwon lafiya da aka samar musu musamman rigakafi, abinci mai gina jiki da kula da lafiyar mata Masu dauke da juna biyu.
Ta kara jaddada kudirin Gidauniyar Aliko Dangote na tallafa wa Kano a kokarinta na ganin dukkan mazauna garin su rayu cikin koshin lafiya.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jihar ta samu gagarumar nasara a fannin kiwon lafiya ga al’ummar jihar.
A cewarsa, gwamnatinsa ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen sake fasalin fannin kiwon lafiya a jihar, duk da inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da manyan asibitoci, da Kuma samar da kwararrun ma’aikata da za su gudanar da su.
Ganduje ya lura da cewa sanya hannu kan takardar yarjejeniyar lafiya ta tabbatar da jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta harkokin kiwon lafiya.
Ya kuma ba da tabbacin jihar ta gaggauta bayar da gudunmawar kudaden da ake bukata domin samun nasarar shirin.