Home Ƙasashen waje Girgizar ƙasa: Saudiyya za ta tallafa wa Turkiyya da dala biliyan 5

Girgizar ƙasa: Saudiyya za ta tallafa wa Turkiyya da dala biliyan 5

0
Girgizar ƙasa: Saudiyya za ta tallafa wa Turkiyya da dala biliyan 5

Saudiyya ta ce za ta saka dala biliyan biyar a babban bankin Turkiyya domin tallafa wa tattalin arzikin kasar.

Sanarwar da Saudiyya ta ftar ta ce gudumuwar wata shaida ce kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A bara ne aka sasanta shugaba Rajib Dayyib Erdowan da yerima mai jiran gado sarautar Saudiyyar Mohammed Bin Salman bayan tsawon shekarun da dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu.

A shekarar 2018 aka kashe Jamal Khashogi a birnin Santabul wanda dan kasar Saudiyya ne kuma dan jarida mai sukar gwamnatin Saudiyyar wanda Tukiyya ta dora alhakin mutuwarsa akan shugabancin Saudiyya.

Turkiyya na matukar bukatar tallafi bayan girgizar ƙasa da ta afkawa ƙasar a makon da ya gabata.