Home Ƙasashen waje Girgizar kasa ta hallaka mutum 42 a India

Girgizar kasa ta hallaka mutum 42 a India

0
Girgizar kasa ta hallaka mutum 42 a India

 

Masu aikin ceto a jihar Manipur a arewa maso gabashin India na can suna bincike domin gano mutum 20 da suka ɓata, kwanaki bayan wata girgizar ƙasar mai ƙarfi da aka yi.

Sama da mutum 40 suka mutu a girgizar ƙasar ya zuwa yanzu, wadda kuma ta lalata wani ɓangare na wata tashar jiragen ƙasa.

Yawancin waɗanda lamarin ya rutsa da su leburori ne da kuma mambobin ƙungiyar sa-kai na sojojin India.

Hukumoi sun ce mamakon ruwan sama da afkuwar wata girgizar ƙasa sun kawowa aikin ceto cikas.

Mamakon ruwan sama da aka yi ta tafkawa ya janyo ambaliyar ruwa a jihohi da ke arewa maso gabashin India, musamman ma jihohin Assam da Manipur da Meghalaya da kuma Tripura.

Hakan ya kawo tasiri sosai a jihar Assam, inda sama da mutum 150 suka mutu sakamakon ambaliya da girgizar ƙasa da daidaita miliyoyin mutane.

An ceto mutum 18 da rai daga wajen da lamarin ya faru a karshen mako. Sai dai jami’ai da ke wajen sun fada wa BBC cewa ‘ikon Allah’ ne kawai zai ceto mutane da yawa.