
Wasu yara su uku, uwa ɗaya uba ɗaya sun mutu a ranar Litinin bayan da gobara ta kone gidan da su ke mai hawa daya da ke unguwar Kabuga, Yan Azara a jihar Kano.
Wani ganau mai suna Ibrahim Lawan, da ke zaune a maƙwabtan gidan ya shaida wa jaridar Punch cewa gobarar ta tashi ne daga dakin farko, inda ya kara da cewa rashin sanar da jami’an kashe gobara a kan lokaci ya sa wutar ta bazu zuwa gidajen da ke makwabtaka da su.
Ya bayyana sunayen wadanda lamarin ya shafa da Fatima Isyaku mai shekaru 16, Abdulsamad Isyaku mai shekaru 15 da Saddika Isyaku mai shekaru 6.
“An kwaso dukkan wadanda abin ya shafa a sume amma daga baya aka tabbatar sun mutu, kuma an mika su ga iyayensu,” in ji Lawan.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:40 na dare daga wani Marwan Umar, wanda ya kai rahoton faruwar gobarar a Kabuga Yan Azara.
A cewar sanarwar, jami’an kashe gobara sun taso daga babban ofishin kashe gobara, inda su ka isa wurin da misalin karfe 10:50 na dare, inda ‘yan kwana-kwana suka samu wani gini mai gidaje biyu da ke ci da wuta.
Ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba kawo yanzu.