
Wata gobara da ba’a san musabbabinta ba ta kone sakatariyar karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi, masu aiko da rahotanni sun bayyana cewar gobarar ta lashe dukkan wasu gine gine dake cikin Sakatariyar, yayin da har ya zuwa yanzu babu labarin musabbabin tashin wannan gobara.