
Daga Hassan Y.A. Malik
Wata gobara ta cinye akalla tanti 300 a wani sansanin ‘yan gudun hijirar da ke karamar hukumar Mafa cikin jihar Borno.
Gobarar ta fara ne da misalin karfe 5:30 na yammacin yau Talata, kuma ta cinye gaba daya sansanin wanda ya samar da matsuguni ga daruruwan ‘yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba su da matsugunnansu.
Wani shaidar gani da ido, Bukar Abba, ya bayyana cewa wutar ta yi saurin ruruwa sakamakon iska mai karfi da ake yi a lokacin da gobarar ke ci.
Bukar ya kara da cewa wutar ta cinye tanti-tanti da aka kafa a sansanin da bukkoki da suturu da sauran kayan amfanin cikin gida na yau da kullum, amma ba a samu salwantar rai ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a san mene ne ya haddasa gobarar ba. Sai dai wannan gobara ta sanya iyalan da abin ya shafa su kwana a waje
Bukar ya yi kira ga gwamnati da sauran kungiyoyin agaji da su gaggauta kawo dauki ga mutanen da ke wannan sansani da wuta ta cinye