
Da sanyin safiyar Litinin din nan ne, wata katafariyar Gobara da ta tashi a kauyen Abanderi dake yankin karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa tayi sanadiyar konewar gidaje 36 da Rumbuna 46 da kuma Akuyoyi 40 a cewar ‘yan Sanda.
Abdu Jinjiri, Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa, ya tabbatar da faruwar wannan gobara ga manema labarai.
Kakakin yace, gobarar wadda ta tashi da misalin karfe 5 na Asuba, ana kyautata zaton ta samu ne sakamakon kone wani daji dake kusa.
“A yau, da misalin karfe 5 na Asubahi, wannan ibtila’i ya faru a kauyen Abanderi dake yankin karamar hukumar Dutse, ana kuma kyautata zaton gobarar ta tashi ne sakamakon kone wani daji dake kusa”
“A sabida haka, a dalilin wannan ibtila’i, gidaje 36 sun kone, da Rumbu dake dauke da hatsi kusan guda 40 duk sun kone, da kuma dabbobi da suka hada da AKuya da Tinkiya kusan 40 duk sun kone kurmus” A cewar Abdu Jinjiri.
Sai dai kuma, ya tabbatar da cewar babu ko mutum guda da ya rasa ransa a sanadiyar wannan gobara.
“Abin godiya ga Allah, shi ne babu hasarar rai ko na mutum guda a wannan ibtila’i, duk da cewar tuni aka kaddamar da binciken ko akwai wani wanda ya rasa ransa, tuni dai harkoki suka koma yadda suke a kauyen da abin ya auku” Inji Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Jigawa.
NAN