
Jam’iyyar PDP ta kafa wani kwamiti da zai tantance wanda zai yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa mataimaki a zaɓen 2023 mai zuwa.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a yau Laraba a Abuja.
Ologunagba ya ce kafa kwamitin tantance ƴan takarar shugaban kasa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa, NWC ya yi, ya bi sashe na VI, sakin layi na 14 na ka’idojin zabe na PDP.
A cewarsa, Chif Tom Ikimi ne zai zama shugaban kwamitin, yayin da Dakta Akilu Indabawa zai yi aiki a matsayin sakatare da Sunday Omobo a matsayin sakataren gudanarwa.
Sauran mambobin da aka amince su yi aiki a kwamitin sun hada da Captain Idris Wada, Cif Osita Chidoka, Binta Bello, Cif Mutiat Adedoja, Austin Opara, Farfesa Aisha Madawaki, Ayotunde George-Ologun, Cif Chidiebelu Mofus da Fidelis Tapgun.
Idan ba a manta ba, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta gargaɗi jam’iyyun siyasa cewa za ta rufe tashar ta na ‘yan takara a zaben 2023 kai tsaye da karfe 6 na yammacin ranar 17 ga watan Yuni domin zaben kasa da kuma karfe 6 na yamma ranar 15 ga watan Yuli.