Home Siyasa 2023: Goodluck Jonathan ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su zaɓi shugabanni nagari

2023: Goodluck Jonathan ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su zaɓi shugabanni nagari

0
2023: Goodluck Jonathan ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su zaɓi shugabanni nagari

 

A yau Alhamis ne tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su zaɓi shugabanni na gari a zaben 2023 domin tabbatar da sahihin mulkin dimokaradiyya a kasar.

Jonathan ya yi kiran ne yayin da ya ke zanta wa da manema labarai a Minna,8 jim kadan bayan ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar a gidansa.

Ya ce ta yin hakan ne kawai manufofin da ake so na samun shugabannin da za su kula da albarkatun kasa za su tabbata.

Jonathan ya ce ya kamata ƴan Nijeriya su yi tunani da kyau su zaɓi wanda zai yi musu hidima a 2023.

Ya ce akwai bukatar ƴan Nijeriya su zaɓi wanda zai yi musu hidima da kyau kuma ba zai saka buƙatar shi a sama da ta ƙasa ba.

Jonathan ya ce: “Dukkanmu muna yi wa kasarmu fatan alheri. Ga kowane dan Najeriya, musamman matasa, zabe na zuwa.

“Dole ne su zaɓi wanda suke ganin zai jagorance mu da kyau, wanda zai yi mana hidima mai kyau.

“Shugaba bawa ne, kuma a matsayinka na shugaban kasa, kai ne ke jagoranci kuma ka yi hidima,” in ji shi.