Home Labarai An gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Neja

An gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Neja

0
An gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Neja

Yansanda sun harba bindiga domin tarwatsa ɗaruruwan mutane a Minna, babban birnin jihar Neja da ke yin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Nijeriya.

Daily Trust ta rawaito cewa tun da misalin karfe 7 na safiyar yau Litinin ne wasu gungun mata su ka tare hanyar Minna zuwa Bida a babban titin Kpakungu domin nuna bacin ransu kan tsadar kayan abinci da masarufi a ƙasa.

Zanga-zangar ta zo ne yayin da a Kano, ake siyar da buhun sukari mai nauyin kilogiram 50 a kasuwar Singer a kan Naira dubu 73,000 sabanin Naira dubu 62,000 da ake siyar da shi a farkon watan Janairu.

Matan na tsaka da zanga-zangar ne sai daga baya wasu mgungun maza suka bi sahun su, inda suka hana ababen hawa tafiya.

Kokarin da ƴansandan suka yi na shawo kan jama’a ya kusan haifar da tashin hankali yayin da masu zanga-zangar suka nemi ƴansandan da su bar wajen, lamarin da ya tilastawa ‘yan sandan harbin iska da dama.

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki matakin rage wahalhalun da talakawan Najeriya ke fuskanta. Al’amura sun lalace sosai,” inji shi.

Daily Trust ta ce ta gaza samun Kakakin rundunar yansandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, a lokacin hada wannan rahoton.