
Hausa wa su kan ce “ba karen da ba bara ba”, bayan da rahotanni su ka baiyana cewa shima sabon Akanta-Janar na rikon ƙwarya, Anamekwe Nwabuoku, akwai zarge-zarge na cin hanci da rashawa a kan sa, inda tuni ma ashe ya na ƙarƙashin bincike a hukumar EFCC.
A tuna cewa a juya Lahadi ne a ka naɗa Nwabuoku a matsayin Akanta-Janar na riƙon ƙwarya bayan da a ka dakatar da Ahmed idri, wanda ya shiga hannun EFCC kan zargin sama-da-faɗi da Naira biliyan 80.
Sai dai kuma wata jarida mai suna Economic Confidential ta bankaɗo cewa ashe Akanta-Janar ɗin na rikon kwarya shima akwai zarge-zarge na cin hanci a rataye abwauyan sa.
Rahoton ya bayyana cewa Nwabuoku ya yi wa kansa da kansa aringizon kuɗaɗe a ma’aikatun da ya riƙe.
Jaridar ta kuma jiyo cewa tuni ma hukumomin yaƙi da cin hanci su ka kwace wasu da ga cikin kadarorin da ya mallaka.
Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa laifin mafi girma da ya aikata shi ne yadda ya riƙa satar kuɗaɗe a lokacin ya na Daraktan Kuɗaɗe da Asusu a Ma’aikatar Tsaron Ƙasa, inda a ka ce ya azurta kansa da kuɗaɗen da a ke ware wa harkar tsaro na cikin gida.
Sannan jaridar ta bankaɗo cewa ya aikata almundahanar kuɗaɗe da dama a ma’aikatu da dama da ya riƙe.
Saura ƴan watanni ƙalilan Nwabuoku ya kai shekarun yin murabus a aiki.