Home Labarai Guduwa Stella Oduah ta yi ba ta kammala bautar ƙasa ba — NYSC

Guduwa Stella Oduah ta yi ba ta kammala bautar ƙasa ba — NYSC

0
Guduwa Stella Oduah ta yi ba ta kammala bautar ƙasa ba — NYSC

 

 

Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC ta ce tsohuwar ministar sufurin jiragen sama kuma sanata mai wakiltar Anambra ta Arewa, Stella Oduah, ba ta kammala bautar ƙasa ba da ɗalibai ke yi idan sun kammala karatun digiri a jami’a.

A wata wasiƙa da ke amsa bukatar kungiyar ‘Concerned Anambra North Peoples Democratic Party Stakeholders’, ta neman tabbatar da ikirarin da Oduah ta yi na cewa ta jefar da shaidar kammala NYSC ɗin ta, Darakta Janar na NYSC ya ce duk da cewa an shigar da Oduah cikin waɗanda za su yi bautar ƙasa a shekarar 1982/83 kuma har a ka kai ta Jihar Legas, sai ta gudu bayan kammala zaman sansani na makonni uku, inda da ga nan ba ta ci gaba da shirin ba ballantana ta kammala shi.

“Sakamakon hakan shi ne ba ta cancanci ba da takardar shaidar kammala yi wa kasa hidima ba”, Darakta Janar ya rubuta a cikin wasikar da Eddy Megwa ya sanya wa hannu a madadinsa.

Jaridar Daily Trust ta samun ganin wasikar, mai kwanan wata 24 ga Mayu, 2022, mai lamba NYSC/DHQ/PPRU/783/VILIII.

A shekarar 2014, ne dai Odua ta samu shaidar kotu da ta ƴan sanda inda ta bayyana cewa a wani lokaci a shekarar 2010, a lokacin da ta ke wucewa daga Akili a Ƙaramar Hukumar Ogboru zuwa Abuja, ta gano cewa wasu kayanta sun ɓace ciki har da shaidar kammala shirin bautar ƙasa ta1983.

Sai dai kungiyar Concerned Anambra North Peoples Democratic Party Stakeholders sun rubuta wa Darakta Janar na NYSC da ya ba su takardar shaidar kammala bautar ƙasa da Stella Adaeze Oduah ta ce ta yi a shekarar 1982/83.

A baya dai ƙungiyar ta rubutawa shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa wasika cewa ya umurci Oduah da ta gabatar da takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC ko kuma a kore ta daga shiga zaben fidda-gwani na jam’iyyar a zaben Sanata ta Arewa.