
A ci gaba da sauraron shari’a tsakanin gwamnatin tarayya da shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Bukola Saraki a kotun da’ar ma’aikata da gwamnati ta gurfanar da Saraki kan batun boye hakikanin abinda ya mallaka a takardar da ya cike na bayyana kadarorinsa kafin a zabe shi, Saraki a zaman na jiya ya jefa wasu maganganu a habaice ga kotun da’ar ma’aikata Code of Conduct Tribunal CCT da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da kuma gwamnatin Buhari.
In ba a manta ba dai, Saraki na gaban wannan kotu ne bisa laifin boye hakikanin kadarorinsa a lokacin da ya zo cike takardar kadarori da masu rike da mukaman gwamnati ke yi, kuma wannan shari’a na gaban CCT tun a watan Yuni na shekarar 2015, bayan da Saraki ya zama shugaban majalisar dattawa ba tare da son jam’iyyarsa ta APC ba.
Ga abubuwan da ya ce:
- Ina mai mika alhinina ga Shugaban wannan kotu ta da’ar ma’aikata, Danladi Umar (wanda a baya shi ke zama akan wannan shari’ar) bisa zargin cin hanci da rashawa akansa da EFCC ta ke yi. In ba a manta ba a manta dai a shekarar 2016 sai da lauyana ya ce Danladi Umar ba shi da ikon sauraren karata saboda shi ma akwai zargin cin hanci da rashawa akansa a gaban EFCC, amma don ya ci gaba da aikin tuhumata, sai nan da nan EFCC ta wanke shi daga zargin da ta ke yi masa a wancan lokacin.
- Abin da matukar daure kai yadda zargin nasa ya sake dawowa sabo bayan wanke Danladi Umar da EFCC ta yi a baya.
- Kamar yadda da dama ‘yan Nijeriya suka sani, gwamnati na zargina ne da laifin rashin bayyana hakikanin darajar kadarata, amma ina so ‘yan Nijeriya su sani cewa dalilan da ke cikin gurfanar da ni a gaban wannan kotu na da alaka da wasu lissafe-lissafe da kutungwuila irin na siyasa.
- Ban sani ba ko makusanta wannan gwamnatin na iya fadawa gwamnatin illar da ayyukanta ke yi akan .yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin nan ke ikirarin wai tana yi.
- Ina da kyakkyawan zato akan bangaren shari’ar kasar nan.