
Jami’an Ƙaramar Hukumar Dambatta a jihar Kano, a jiya Litinin sun ce wata iska mai karfin gaske da ta afku a yankin, ta yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da suka hada da wata mata mai juna biyu da ƙananan yara, bayan ta lalata gidaje 70.
Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Mihammad Abdullahi Kore ne ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar tawagar Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, SEMA, ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren hukumar, Dakta Saleh Aliyu Jili.
Kore ya ce lamarin da ya faru a unguwar Bai da Dukawa, ya kuma yi sanadiyyar lalata gidaje sama da 70 a yankin.
Ya ƙara da cewa majalisar karamar hukumar za ta biya kuɗaɗen maganin waɗanda su sami raunuka, yayin da ya yi alkawarin da5ukar matakan da suka dace don hana afkuwar lamarin nan gaba.
A nasa bangaren, Dakta Jili ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Jili ya ce sun je Dambatta ne a madadin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje domin jajanta wa iyalan wadanda bala’in ya shafa tare da basu kayan agaji.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar kano ta hanyar fito da managartan tsare-tsare wadanda za su taimaka wajen cigaban rayuwar al’umma.
Sakataren zartarwa ya ce tawagar za ta mika kayan tallafin ga mataimakin shugaban karamar hukumar Dambatta wanda shi ne shugaban kwamitin bayar da agajin gaggawa na Karamar Hukumar domin rabawa ga wadanda abin ya shafa.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan siminti, kwanon rufi da matashin kai sai katifu, tabarma, kayan abinci da kayan sawa da dai sauransu.