Home Labarai Guguwa ta lalata gidan gonar kaji inda ta kashe guda 3,600 a Plateau

Guguwa ta lalata gidan gonar kaji inda ta kashe guda 3,600 a Plateau

0
Guguwa ta lalata gidan gonar kaji inda ta kashe guda 3,600 a Plateau

Wata mummunar guguwa ta afkawa gidan kaji na Dauda Mafala & Sons da ke Rapomol a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Plateau a ranar Asabar din da ta gabata, inda ta kashe kaji sama da 3,600.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, wanda ya ziyarci gonar a jiya Lahadi, ya gano cewa lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.

Guguwar ta lalata wasu kejinan kaji guda shida, wani bangare na shingen kaji da turakun wutar lantarki, da dai sauran gine-gine a gidan gonar.

Manajan daraktan gidan gonar, Keneth Mafala, ya shaida wa NAN cewa, gidan gonar da aka kafa tun a 1976, ya na da girman da zai dauki kaji dubu 60.

Mafala ya ce guguwar ta kuma lalata wani keji mai sarrafa kansa da kuɗin da ya kai dalar dubu 80,000.

“Da misalin karfe 3:30 na rana a ranar Asabar, guguwar iska ta lalata gine-gine da dama a wannan gona.

“Ta lalata wata rumfar kaji da ke dauke da kaji masu kwanci dubu 10,800.

“A yanzu haka, mun yi asarar tsuntsaye dubu 3,600, kuma kamar yadda kuke gani, muna ci gaba da kwashe wasu.

“Don haka, adadin na iya karuwa zuwa lokacin da za mu kammala,” in ji shi

Da ta ke tsokaci a kan ibtila’in, mai magana da yawun kungiyar masu kiwon kaji ta ƙasa, reshen Plateau, Nanji Gambo ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ta ce babbar asara ce ga sana’ar kiwon kaji a jihar.

Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Plateau da ta yi amfani da wani bangare na tallafin Naira biliyan 5 da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin farfado da sana’ar kiwon kaji a jihar.