
Wata Jarumar masana’antar Kannywood, Amal Umar, ta gurfana a gaban Kotun Majistare mai lamba 24 da ke unguwar Gyadi-Gyadi a cikin birnin Kano, bisa zargin yunkurin baiwa jami’in tsaro cin hanci.
An zargi jarumar da yunkurin bada cin hancin kudi Naira dubu 250 ga wani dan sanda mai suna ASP Salisu Bujama na rundunar ƴansandan Najeriya shiyya ta daya a jihar Kano.
A cewar mai gabatar da kara, zargin cin hancin na da nufin dakatar da binciken ƴansanda kan zargin karkatar da kudade da saurayin ƴar fim din, mai suna Ramadan Inuwa ya aikata.
Matsalar ta faru ne a lokacin da wani Yusuf Adamu ya shigar da kara ta hannun lauyansa, H.I. Dederi, ga Mataimakin Sufeto Ƴansanda, AIG, Umar Mohd Sanda, a ranar 18 ga Agusta, 2022, inda ya bayyana zargin da ake yi masa na karkatar da wasu makudan kudade da suka kai Naira miliyan 40 a wani cinikin wayar salula.
Koken ya kai ga binciken ‘yan sanda, inda ya nuna cewa Inuwa ya tura Naira miliyan 13 zuwa asusun bankin jarumar Kannywood Amal Umar.
A cewar kakakin rundunar ƴansandan Najeriya shiyya ta daya a Kano, CSP Bashir Muhammed, daga nan ne aka gayyaci jarumar domin amsa tambayoyi, inda daga bisani kuma aka bada belin ta, amma ba a bari ta tafi a cikin motar da yazo da ita ba bisa zargin cewa saurayin na ta ne ya saya mata.