Home Labarai An gurfanar da makanike a kotu bisa zargin sace motar kwastoma

An gurfanar da makanike a kotu bisa zargin sace motar kwastoma

0
An gurfanar da makanike a kotu bisa zargin sace motar kwastoma

 

 

 

An gurfanar da wani makanike mai suna Stanley Collins a yau Laraba a babbar kotun majistire a Kaduna bisa zargin sace motar kwastoman sa kirar Honda Shuttle wacce kuɗin ta ya kai naira dubu 980.

Tuni dai kotun ta tuhumi Collins da laifin sata, inda shi kuma ya musanta.

Dan sanda mai ƙara, Sifeto Chidi Leo, ya shaida wa kotu cewa wanda a ke ƙara ya taka laifin ne a ranar 10 ga watan Febrairu da misalin ƙarfe 10 na dare.

Ya ce wanda a ke ƙara ya sace motar, mallakin wani Paul Gabriel da ya kai masa ita domin gyara wa.

Leo ya ƙara da cewa wanda a ke ƙarar ya sace motar ne ya kuma sayar da ita, amma sai ya ce wai sace wa a ka yi da tsakar dare.

Sai Leo ya ƙara da cewa an gano motar nan ta amfani da na’urar bin sahu wato ‘tracker’.

Ya ce laifin ya saɓa da sashi na 287 na dokar penal code ta Kaduna.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Emanuel ya bada belin wanda a ke ƙara kan Naira dubu 200 da kuma wadanda za su tsaya masa mutum biyu.