Home Labarai An gurfanar da tsohon shugaban ABU da ma’ajin jami’ar bisa zargin badaƙalar biliyan 1

An gurfanar da tsohon shugaban ABU da ma’ajin jami’ar bisa zargin badaƙalar biliyan 1

0
An gurfanar da tsohon shugaban ABU da ma’ajin jami’ar bisa zargin badaƙalar biliyan 1

An gurfanar da Farfesa Ibrahim Garba da Ibrahim Shehu Usman tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a gaban mai shari’a A.A Bello na babbar kotun jihar Kaduna, bisa tuhume-tuhume takwas da su ka hada da sata da kuma karkatar da kudade har Naira biliyan 1.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ce ta EFCC ta gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu.

Shari’ar dai ya biyo bayan bincike na ƙarƙashin ƙasa na tsawon watanni da aka gudanar bayan wani korafi da a ka yi, inda ake zargin mutanen biyu da karkatar da kuɗaɗen da aka tanada don gyaran otal din taro na Kongo, Zariya.

Binciken ya tabbatar da cewa wadanda ake tuhumar sun sace sama da Naira biliyan daya daga asusun ajiyar jami’ar tare da karkatar da su zuwa asusunsu na sirri.

Sai dai kuma sun musanta tuhumar da ake musu, lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.

Mai shari’a Bello ya bayar da belin wadanda ake tuhuma a kan kudi Naira miliyan 10 kowanne da kuma wanda zai tsaya musu a daidai wannan adadi, wanda dole ne ya mallaki kadarorin da ke karkashin ikon kotun.

Haka kuma za su ajiye fasfo dinsu na kasa da kasa a gaban magatakardar kotun.

An dage sauraren karar har zuwa ranar 15 da 16 ga Maris, 2023 domin shari’a.