
Wani magidanci mai shekaru 42, Austin Anthony, a ranar Talata ya tsaya a wata kotun majistare da ke Ikeja bisa zarginsa da cin zarafin matarsa tare da raunata jaririnsa ɗan wata uku a hannu.
A na tuhumar wanda ake karar, mai sana’ar gasa burodi, wanda ke zaune a gida mai lamba 16, layin Ajibade, Baruwa Ipaja a jihar Legas,da laifin cin zarafi, wanda ya haifar da mummunar illa da barazana ga rayuwa.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ASP Raji Akeem, ya shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Satumba a gidan wanda ake kara.
Akeem ya ce faɗa ne ya ɓarke tsakanin wanda ake kara da matarsa, Ifeyinwa, kan gazawar mutumin na daukar nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na miji da kuma uba ga ‘ya’yansu.
Akeem ya ce wanda ake tuhumar da karfi ya cire jaririn nasu dan wata uku daga bayan mahaifiyarta kuma a cikin haka; jaririn ya samu rauni a hannunta.
Mai gabatar da kara ya kuma ce wanda ake karar ya lakaɗa wa mai ƙarar dukan tsiya tare da turo ta daga wani bene zuwa ƙasa.
“Hakan ya sa ta kareraye a kafafunta kuma ta samu munanan raunuka a jikinta,” in ji shi.
Akeem ya kuma ce wanda ake tuhumar ya yi barazanar kashe matar ta sa da wukar kicin.
Laifukan, a cewar mai gabatar da kara, sun saɓa da sashe na 56, 172, 245 da 246 na dokokin laifuka na jihar Legas, na 2015.
Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta laifin da ake tuhumar sa da shi.
Alkalin kotun, B. O. Osunsanmi, ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N500,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
Osunsanmi ta ɗage sauraron karar har zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba.