Home Labarai An gurfanar da wata mata a kotu bisa yaɗa kazafi a TikTok

An gurfanar da wata mata a kotu bisa yaɗa kazafi a TikTok

0
An gurfanar da wata mata a kotu bisa yaɗa kazafi a TikTok

Wata mata ƴar shekara 34, Gift Okpomini, a yau Alhamis an gurfanar da ita a gaban kotun majistare da ke Ikorodu a jihar Legas, bisa zargin ta da yaɗa kazafi a kan wasu ma’aurata a Tiktok.

Ƴan sanda na tuhumar Ms Okpomini, wadda ba a bayar da adireshinta ba, da laifuka uku da su ka shafi halayya da ka iya haifar da ruguza amana, aika abubuwa masu hadari ko batsa ta hanyar wallafa wa da sata.

Sai dai wacce ake tuhumar ta musanta aikata laifin.

Lauyan masu shigar da kara, Insfekta Adegeshin Famuyiwa, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ta aikata laifin a ranar 8 ga watan Nuwamba da misalin karfe 1:29 na rana. a gida mai lamba 4, Erubami str, a yankin Igbogbo na Ikorodu a jihar Legas.

Famuyiwa ya ce wacce ake zargin ta nuna halayya wacce za ta iya kawo rashin zaman lafiya ta hanyar sanya hotunan Mista da Misis Okaweze Osbert a Tiktok Nijeriya, inda ta yi musu lakabi da masu laifi, barayi da ake nema ruwa a jallo kuma ta san hakan karya ne.

Mai gabatar da kara ya kuma ce a tsakanin Agusta 1 zuwa 8 ga watan Agusta, a Ogunlewe str, wacce ake kara ta cinge N67,000 mallakar Gab lotto da kuma kwashe cinikin N5,195 mallakar Wesco lotto.

Laifin, a cewarsa, ya saba wa tanadin sashe na 259 (b), 168 (d) da 287(7) na dokar manyan laifuka ta jihar Legas, 2015.

Alkalin kotun, A.O Ogbe, ya amince da bada belin wacce ake tuhumar kan kudi naira 50,000 tare da wanda zai tsaya mata shima mai dubu 50 da kuma adireshi mai inganci.

Ya ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Disamba.