Home Ƙasashen waje Ɗan gwagwarmayar ƙwato ƴancin baƙaƙe a Afirka ta Kudu, Desmond Tutu ya rasu

Ɗan gwagwarmayar ƙwato ƴancin baƙaƙe a Afirka ta Kudu, Desmond Tutu ya rasu

0
Ɗan gwagwarmayar ƙwato ƴancin baƙaƙe a Afirka ta Kudu, Desmond Tutu ya rasu

 

Fitaccen ɗan gwagwarmayar nan ta ƙwato ƴancin baƙaƙe a Afirka ta Kudu, Acibishof Desmond Tutu ya rasu.
Fadar Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu ce ta sanar da rasuwar Tutu, wanda ya lashe kyautar gwarzon zaman lafiya ta duniya.
Fadar ta ce Acibishof Tutu ya rasu a yau Lahadi ya na da shekaru 90 da haihuwa.
Kawo yanzu dai fadar shugaban kasar ba ta baiyana abin da ya haifar da rasuwar ta sa ba.
Sai dai kuma tun a shekarar 1990 likitoci su ka gano ya kamu da cutar jeji, inda ya sha fama da jigilar asibiti a kan ciwon.
A shekarar 1984 ne dai a ka baiwa Tutu kyautar gwarzon zaman lafiya sakamakon gwagwarmayar yaƙi da kin jinin bakake ba tare da wata rigima ba.