
Rundunar ƴan sanda a jihar Legas a yau Asabar ta ce binciken gawar Ifeanyi Adeleke, ɗan mawaƙin nan Davido da amaryarsa, Chioma Rowland, ya bayyana cewa ya yaron ya mutu ne a ruwa.
Jaridar Punch ta rawaito jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar.
Hundeyin ya ce, “An kammala gwajin gawar kuma sakamakon ya tabbatar da cewa yaron (Ifeanyi) ya nutse wa ya yi a ruwa.”
Tun a baya a ka bayyana cewa akwai yiwuwar ƴan sanda su gudanar da bincike don gano ko Ifeanyi ya mutu ne sakamakon nutsewa a cikin wani ruwa da ke gidan mahaifinsa da ke unguwar Banana Island a jihar Legas.
Wata majiya mai tushe wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce yana cikin ɓangaren ayyukan ƴan sanda su gudanar da binciken gawa a irin wannan yanayi, ta kuma kara da cewa idan iyalan mamaci ba su amince da yin gwajin ba to sai ƴan sandan su hakura.