Home Labarai Gwamna Abba ya ɗauki nauyin rayuwar marayu 95 a Kano

Gwamna Abba ya ɗauki nauyin rayuwar marayu 95 a Kano

0
Gwamna Abba ya ɗauki nauyin rayuwar marayu 95 a Kano

A wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da daukar nauyin rayuwar marayu 95 a Kano.

Gwamnan ya sanar da wannan abun alheri ne a lokacin liyafar cin abinci ta musamman tare da marayun 95 a gidan marayu na jihar tun bayan da iyayensu su ka rasu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakintofa, ya fitar, ta ce Yusuf ya ayyana cikakken ɗaukar nauyin rayuwar marayu 95 daga yanzu.

“Ina so in sanar da cewa mun dauki nauyin dukkan marayu 95 da ke zaune a wannan gida, za mu dauki nauyin karatunsu tun daga firamare har zuwa manyan makarantu, lafiyar su, cin su da shan su da sauran bukatu na yau da kullum har tsawon mulkina”.

“Yanzu ku ‘ya’yana ne, zan kula da ku a matsayin nawa, za ku fara jin dadin rayuwa in sha Allahu” gwamnan ya tabbatar.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa har zuwa karshen wa’adin mulkin sa, za a dauki marayun a matsayin mutane masu matukar muhimmanci tare da cikakken amfani, kulawa da gata. Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta bai wa yaran damar kaiwa ga gaci a rayuwarsu.