Home Labarai Gwamna Ayade ya rufe kofar gidan gwamnati domin kamen ƴan latti

Gwamna Ayade ya rufe kofar gidan gwamnati domin kamen ƴan latti

0
Gwamna Ayade ya rufe kofar gidan gwamnati domin kamen ƴan latti

 

A yau Laraba ne dai Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade ya kulle kofar gidan gwamnati ga ma’aikata da dama a ofishin Gwamna saboda rashin zuwa aiki da wuri.

Gwamnan ya isa ofishin da misalin ƙarfe 8 na safe, inda da ƙarfe 8:30 na safe ya bayar da umarnin rufe kofar, hakan ya sanya ma’aikata da dama su ka yi cirko-cirko a bakin kofar shiga hankali a tashe.

Da yawa daga cikin ma’aikatan sun yi mamakin umarnin da Gwamnan ya bayar domin a tunaninsu, har yanzu yana kasar waje bayan wata daya na wata tafiya ta neman zuba jari a jihar da ya yi.

Da yawa daga cikin ma’aikatan da suka zanta da jaridar The Nation, sun ce basu da karsashin zuwa aiki saboda rashin jin dadi da walwalar aiki.

Shugaban ma’aikatan, Mista Timothy Akwaji ya ce an dauki matakin ladabtar da ma’aikatan ne sakamakon latti.