
Gwamna Abubakar Bello na Jihar Naija ya dakatar da shugaban Hukumar kula da Ilimin Bai-ɗaya ta jihar, Isah Adamu bisa wasu badaƙaloli wajen tafiyar da hukumar.
Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane.
Matane ya ƙara da cewa “wasu badaƙaloli da aka gano a cikin ayyukan hukumar ne suka tilasta dakatarwar,”
Gwamnati ta umurci Adamu da ya mika al’amuran hukumar ga mamba na dindindin na III a hukumar domin ba da damar yin garambawul a ayyukanta domin samun ci gaba.