Home Kanun Labarai Gwamna El-Rufai ya tsinewa Sanatocin Kaduna, yace ba su da amfani

Gwamna El-Rufai ya tsinewa Sanatocin Kaduna, yace ba su da amfani

0
Gwamna El-Rufai ya tsinewa Sanatocin Kaduna, yace ba su da amfani

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru EL-Rufai ya kasa jurewa akan kin amincewa da Sanatocin Kaduna suka yi a majalisar dattawa na ciwo bashin dala miliyan 350 a bankin Duniya, a yayin wani gangani na gudanar da zaben kwangires na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Gwamna El-Rufai ya fito fili ya tsinewa sanatocin Kaduna uku.

“Sanatocin da muke da su a jihar Kaduna ba su da wani amfani, Shehu Sani da Sule Hunkuyi da Laah duk Allah ya tsine musu albarka, domin basu amfanawa jihar Kaduna komai ba”

“Wadannan Sanatocin sune makiyan jihar Kaduna, makiya cigaban talakawa, basa son suga ana yiwa al’umma aiki, saboda muguntarsu da mugun nufinsu yasa suka kawo tarnaki ga batun bashin da zamu ciwo domin muyi muku ayyukan tituna da asibitoci da sauransu”

“A yau al’ummar jihar Kaduna ba su da wasu makiya da suka wuce Sanata Shehu Sani da Suleiman Hunkuyi da Danjuma Laah, ina yi musu mummunan fatan a karshensu, tsinannu” A cewar Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.