Home Labarai Gwamna Ganduje ya sanya hannu a kasafin kuɗin shekara ta 2022

Gwamna Ganduje ya sanya hannu a kasafin kuɗin shekara ta 2022

0
Gwamna Ganduje ya sanya hannu a kasafin kuɗin shekara ta 2022

 

A yammacin Talatar nan ne Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kasafin kuɗin shekara ta 2022 wanda Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta Amince da shi.

Gwamnan ya sanya hannun ne yayin taron Majalisar Zartarwar ta Jihar Kano Wanda ya gudana a dakin taro na Africa House.

A jawabinsa bayan ya rattaba hannun, Ganduje ya yabawa Ƴan Majalisar bisa yadda su ka yi aikin kasafin kuɗin ba tare da ɓata lokaci ba, wanda, a cewarsa, hakan zai baiwa gwamnatin damar fara amfani da kasafin kuɗin a farkon sabuwar shekara tunda ya zama doka.

Ganduje ya ce gwamnatin sa za ta yi gaggawar fara aiki da kasafin kuɗin, wanda mafi yawan sa manyan aiyuka ne, inda ya ce kwanan nan al’ummar jihar su ci gaba da ganin manya-manyan aiyuka.

Gwamna Ganduje ya ce zai tabbatar an yi aikin da kasafin kuɗin kamar yadda majalisar ta amince da shi.

Ganduje ya yi alkawarin cigaba da baiwa majalisar ƴancin cin gashin kan ta ba tare da tsoma baki a harkokin aikinta ba.

Ya kuma yaba da yadda majalisar ta gudanar da taron jin ra’ayoyin al’umma,Inda ya bada tabbacin kasafin kuɗin zai fi mai da hankali wajen kammala aiyukan da suka fara don gudun barin bashi mai yawa ga gwamnatin da zata gaje shi, Inda ya ce kasafin kuɗin ya samu ƙari daga sama da Naira Biliyan 190 zuwa sama da Naira Biliyan 200.

A Jawabinsa tun da fari l, Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari ya ce sun samu nasarar kammala aikin nasu ne akan lokaci sabo da yadda Gwamnan ya gabatar musu da daftarin kasafin a kan Lokaci.

Chidari yace kuma dukkanin Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Jihar Kano sun bayar da duk wani haɗin kai ga kwamitocin Majalisar wanda hakan ya taimaka wajen Samun nasarar aikin kasafin kudin kamar yadda doka ta basu dama.

Ya Kuma baiwa Gwamnan tabbacin shugabancin Majalisar ƙarƙashin sa zai cigaba da baiwa ɓangaren zartarwar hadin kai domin samun nasarar yi wa al’ummar jihar kano aiyukan cigaba.