Home Labarai Gwamna Lalong ya nemi afuwa kan zarginsa da ‘saɓo’

Gwamna Lalong ya nemi afuwa kan zarginsa da ‘saɓo’

0
Gwamna Lalong ya nemi afuwa kan zarginsa da ‘saɓo’

 

 

Gwamnan Plateau, Simon Lalong ya nemi afuwan mabiyan cocin Katolika kan kalamansa da suka jawo ce-ce-ku-ce lokacin da ya ke kare matsayar nadin da jam’iyyarsa ta APC ta yi ma sa.

Tun a ranar Talata aka soma wata takaddama tsakanin Gwamnan jihar Filato Simon Lalong da Mabiya addinin Kirista ‘yan darikar Katolika.

Hakan ya biyo bayan kalaman da gwamnan ya yi cewa Fafaroma Francis bai ga laifin karbar mukamin darakta-janar na kamfe din ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, ba duk da cewa dukkansu Musulmai ne.

Kalaman sun fusata kiristoci mabiya katolika wadanda suka bayyana ambato sunan Fafaroma a zaman raini ga jagoran nasu.

Abin da ya kai ga sun bukaci a gaggauta dakatar da Lalong daga harkokin cocin.

Sai dai a wata wasika da ya aike wa cocin, Lalong ya amsa cewa ya yi kuskure don haka ya nemi a yafe ma sa, da alkawarta ci gaba da ayyukansa ta hanya mafi dacewa.

Gwamna Lalong ya ce bai yi wadannan kalamai ba domin muzanta kiristocin kasar.