
Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya bayyana aniyarsa ta yin takarar Sanata a jihar Zamfara.
Tsohon Gwamnan jihar Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura shima ya fito yankin daya da Gwamna Yari, abinda yake nuna cewar zasu nemi kujerar Sanata guda tare da tsohon maigidan Yarima.
Alamau na nuna cewar akwai jikakkiya tsakanin Gwamnan jihar mai ci Abdulaziz Yari da kuma tsohon Gwamna Sanata Yarima.
Domin ko a jiya Gwamna Yari ya bayyana goyon bayansa ga takarar Gwamnan jihar ya kwamishinansa na kudi, sabanin mataimakinsa Ibrahim Wakkala da aka ce Yarima na marawa baya.