
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya zaɓi Hajiya Jamila Dahiru, Malama a sashen Ilimin sadarwa na Mass Communication a Jami’ar Ahmadu Bello, ABU, Zariya, domin naɗa ta a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartaswa ta jihar Bauchi.
Haka kuma gwamnan jihar ya zaɓo Amina Muhammad Katagum domin naɗa ta a matsayin Kwamishina.
Dukkan ‘yan takarar biyu dai majalisar dokokin jihar za ta tantance su a ranar Talata, 13 ga watan Disamba.
Mrs Dahiru, tsohuwar ɗalibar jami’ar Bayero, BUK, wata kwararriya ce a fannin yaɗa labarai kuma mai fafutukar ci gaban mata, ta fito daga karamar hukumar Toro, yayin da Katagum ta fito daga karamar hukumar Zaki ta jihar.
Nadin na kunshe ne a cikin wata wasika da gwamnan ya aike wa majalisar, wadda shugaban masu rinjaye na majalisar, Tijjani Muhammad Aliyu ya gabatar da shi ga shugaban majalisar, Abubakar Suleiman, a zaman taron na ranar Alhamis.
Ya ce shugaban masu rinjaye ya gabatar da kudirin cewa mutanen biyu da aka zabo su bayyana a gaban majalisar wakilai a ranar Talata 13 ga Disamba, 2022 don tantancewa.
A cewar sanarwar, shugaban marasa rinjaye, Bakoji Aliyu Bobbo ne ya goyi bayan kudurin.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa za a iya nada daya daga cikin matan a matsayin kwamishinan ilimi bayan murabus din Dr Aliyu Tilde kwanan nan.