
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya umurci ciyamonin Kananan Hukumomi 20 da mataimakansu da kansiloli da sakatarorinsu da su ajiye mukamansu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar a Bauchi a jiya Asabar.
A cewar, Gidado, umarnin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin shugabannin majalisar a ranar 10 ga Oktoba, 2022.
Ya ce an umurci jami’an da abin ya shafa da su mika al’amuran ofisoshinsu ga shugabannin sashen gudanarwa daga Talata 11 ga watan Oktoba, har sai an gudanar da sabon zaɓe ko kuma naɗa shugabanni na riƙon ƙwarya.
Mai taimaka wa gwamnan ya ce matakin ya biyo bayan biyayya ga sashe na 2 (i) na dokar kafa wa da gudanar da kananan hukumomi na jihar Bauchi na shekarar 2013, bayan an yi mata kwaskwarima.
“Mai girma gwamna, ya gode wa ciyamomi da masu barin gado da mataimakansu, kansiloli, da sakatarorin gwamnati bisa ayyukan da ake yi wa jihar tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba,” in ji sanarwar.