
Gwamnatin jihar Bayelsa ta baiwa dukkan jami’an tsaron jihar umarnin da su binciko tare da kamo wanda suka kashe mashahurin mahaucin nan na jihar Alhaji Jibril Abdulkarim tare da wasu mutum uku da aka samu wasu mutane suka halaka su.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar mahaucin tare da uku daga cikin ma’aikatansa sun mutu ne, sakamakon harbin da wasu mutane da ba’a san ko su waye ba suka yi musu a mayankarsu da ke birnin Yenaguwa a ranar 2 ga watan Disamba.
Alhaji Jibril Abdulkarim yana daya daga cikin memba a kungiyar masu kula tare da kare gandun daji a jihar, kuma shugaban kungiyar mahautan jihar.
Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, a lokacin da ya ziyarci iyalan mamacin ya nuna alhininsa tare da nuna juyayin rashin wannan mutumin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan rashi da suka yi, sannan yayi tur da wadan da suka kai wannan harin.
Gwamna Dickson wanda Shugaban ma’aikatan jihar, Talford Ongolo ya wakilta, ya tabbatarwa da iyalan mamacin cewar hukumomi suna nan suna aiki tukuru wajen ganin an kamo wadan da suka yi wannan kisan.
Ya bayyana cewar, Gwamnati zata hada kai tare da dukkan hukumomin tsaro, domin ganin an bi dukkan hanyoyin da suka dace wajen tabbatar da cewar an kamo wadan da suka yi wannan kisan.