
A yayin da dattawa da shugabanni na jihar Borno suka kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadar Gwamnatin tarayya dake Aso Villa, Gwamnan jihar Borno Kasheem Shettima ya fashe da kuka yayin da yake yiwa Shugaban kasa bayani kan ta’adin ‘Yan kungiyar Boko Haram.