
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada Abdulkadir Abdussalam a matsayin sabon Akanta Janar na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar jiya.
Ya ce Gwamnan ya kuma nada Garba Ahmed-Bichi a matsayin sabon Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano.
A cewar sanarwar, Yusuf ya nada Dakta Rahila Mukhtar a matsayin Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Gudunmawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano, KCHMA.
Hassan Baba Danbaffa kuma an nada shi a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano, KARMA.
Gwamnan ya kuma nada Arc. Ibrahim Yakubu, a matsayin Manajan Daraktan Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA.
Dawakin-Tofa ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da bikin rantsar da wadanda aka nada domin samun damar karbar ragamar aiki nan take.