Home Labarai Gwamnan Kano ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi

Gwamnan Kano ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi

0
Gwamnan Kano ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi 44 nan take.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature ya fitar.

Rushewar tasu na zuwa ne, bayan majalisar dokokin jihar Kano ta kara musu wa’adi zuwa watanni 2, inda wa’adinsu ya kare a ranar 8 ga watan Satumba.

Karin lokacin, acewar ‘yan majalisar an yi shi ne don tabbatar da dorawa a shugabancin karamar hukuma.

An shirya gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano dai ranar 26 ga watan Oktoba.

Abba Yusuf ya umarci tsoffin shugabannin na riko da su mika ragamar jagorancin kananan hukumomin ga daraktocin mulki.

“Wannan rushewar ta shafi dukkan shugabanni da mataimakansu da Sakatarori da Kansiloli”, inji Gwamnan.

Ya bayyana godiya ga shugabannin na riko bisa gudunmawar ra suka bayar wajen ci gaban yankunan su tare da alkawarin yin aiki tare anan gaba.