Home Labarai Gwamnan Kano ya karbe kwangilar aikin titi a Garko daga hannun dan kwangila

Gwamnan Kano ya karbe kwangilar aikin titi a Garko daga hannun dan kwangila

0
Gwamnan Kano ya karbe kwangilar aikin titi a Garko daga hannun dan kwangila

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya soke kwangilar gina titi mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Garko, sakamakon gazawar da dan kwangilar ya yi wajen aikin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gwamna Sanusi Bature D/Tofa ya fitar a Kano,a Litinin din nan.

Sanusi D/Tofa ya rawaito cewa gwamnan ya tabbatar wa al’ummar karamar hukumar cewa “za a nada sabon dan kwangila mai inganci nan da ‘yan kwanaki masu zuwa” domin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci.

Gwamnan ya kuma bayyana kudurinsa na samar da cibiyar kiwon lafiya ta zamani a Garin Garko, da nufin kusantar da harkokin kiwon lafiya ga jama’a.

Ya kuma nuna jin dadinsa da ci gaba da goyon bayan da al’ummar yankin ke bashi, ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da ci gaba da samar musu cigaba.