
Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya kaddamar da shirin baiwa daliban makarantun sakandire na jihar tallafin akuyoyi a baki dayan jihar.
A lokacin da yake kaddamar da shirin a karamar hukumar Dutsin-Ma, Gwamnan wanda kwamishiniyar ilimi Halimatu Idris ta gabatar, tace, Gwamna ya fito da tsarin baiwa daliban sakadire Akuyoyi domin su samu abin dogaro ga kawukansu.
Kwamishiniyar, tace wannan rabon awakin na daga cikin tanade-tanaden Gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari na inganta rayuwar al’umma, da kumai baiwa ilimi muhimmanci a jihar.
Ta kara da cewar, Gwamnati ta ware makarantu guda 20 daga kowacce mazabar dan majalisar dattawa a jihar domin fara bayar da tallafin akuyoyin gare su.
Ko a shekarar da ta gabata, ta sayo awakai guda 4,500 ta rabawa al’ummar jihar a matsayin wani abin dogara da kai.