Home Labarai Gwamnan Katsina, Radda, ya naɗa sabbin muƙamai

Gwamnan Katsina, Radda, ya naɗa sabbin muƙamai

0
Gwamnan Katsina, Radda,  ya naɗa sabbin muƙamai

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya naɗa
Ahmed Dangiwa a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

A wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya wa hannu a jiya Litinin, gwamnan ya kuma nada Jabiru Tsauri a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati; Muhtar Saulawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata da; Abdullahi Turaji a matsayin Babban Sakataren Gwamna.

Sauran nadin da Radda ya amince da su sun hada da Maiwada Danmallam a matsayin Darakta Janar na yada labarai; Ibrahim Kaula Mohammed a matsayin babban sakataren yada labarai; Miqdad Isah a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (kafafen yaɗa labarai na zamani) da; Abubakar Jikamshi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (jarida, rediyo da talabijin).

Gwamnan ya kuma nada Bishir Maikano a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (Protocol) Mataimakin Gwamnan.

Sauran nadin sun hada da Hassan Danhaire a matsayin babban mataimaki na musamman (Special Services) ofishin mataimakin gwamna da Ahmed Rabiu a matsayin mai daukar hoto na gwamna.

Gwamnan ya taya sabbin wadanda aka nada murna, sannan ya bukace su da su hada kai da shi wajen ganin an dawo da martabar jihar.