
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya aike wa Sarki Ohinoyi na Ƙasar Ebira, Abdulrahman Ado Ibrahim, takardar tuhuma bisa ƙin tarbar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ziyarar aiki da ya kai a jihar a ranar 29 ga watan Disamba.
Gwamnatin jihar, a takardar tuhuma da ta aike wa Sarkin, mai ɗauke da sa hannun daraktan harkokin masarautu na jihar, Enimola Eniola, mai kwanan wata 5 ga watan Janairu, ta ce abinda Sarkin ya aikata ka iya zubar da mutuncin jihar Kogi, musamman ma ƙasar Ebira a idon duniya.
Gwamnatin ta suffanta abinda Sarkin ya yi a matsayin rashin biyayya da ɗa’a ga gwamnati.
A takardar, gwamnatin ta buƙaci Sarki Ibrahim da ya bada hakuri a cikin sa’o’i 48 sannan ya faɗi dalili gamsasshe da ya sa ya ƙi zuwa tarbar shugaban ƙasa.