
Daga Hassan Y.A. Malik
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya fitar da sanarwar mayar da kwamishinoninsa da kantomomin kananan hukumomin jihar 21 bakin aikinsu awa daya kacal da sallamarsu daga aiki.
Gwamna Bello bayan samun labarin kama wasu khakin soja da bindigo da hukumae kwastam ta yi kuma aka alakanta wadannan kaya da aka samu da gwamnatinsa, ya umarci kwamishinoninsa da su bar ofisoshinsu da gaggawa kuma su mika duk wani abu da ke hannunsu na gwamnati ga manyan sakatarorin ma’aikatar da suke yi wa kwamishina. Haka suma, kantomomin kananan hukumomin jihar, an umarcesu da su mika mallakin gwamnati da mukullayen ofisoshinsu ga darakta janar na kananan hukumomi.
Sai da sa’a daya bayan korar kwamishinoni da kantomomin ne sai wata sanarwa ta sake fita daga gwamna Yahaya, inda ya sake umartar wadanda ya kora da su koma ofisoshinsu bisa sharadin su sauya halayensu da yadda suke tafiyar da ayyukansu don cimma muradan gwamnatin jihar.
Sanarwar korar kwamishinonin ya janyo dar-dar da fargaba a siyasar jihar, duk kuwa da cewa, alamu sun nuna tun a makon da ya gabata gwamnan na son ya yi juyen kwamishinonin nasa.
Watakila wannan ne ma ya sanya gwamnan ya sake fitar da wata sanarwar na dawo da kwamishinonin, inda ya bayyana cewa kwamishinonin za su ci gaba aikinsu ne bisa umarninsa kadai.
Darakta yada labarai na gwamnan, Kingsley Fanwo ya aikawa da manema labarai ta WhatsApp cewa gwamnan ya sauya ra’ayinsa na korar majalisar zartarwarsa.