
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya naɗa wasu yan kabilar Ibo guda biyu a jihar a matsayin mataimaka na musamman, wato SA.
Sule ya sanar da naɗin ne a yau Alhamis, a lokacin da ƴan ƙabilar Igbo suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Lafia.
Wadanda aka nada sun hada da Chukwuemeka Igwedinma, Mataimaki na Musamman a kan harkar jahohi, da Lovelyn Okechukwu, Mataimakiya ta Musamman a kan Al’adu.
Mutanen biyu suna zaune ne kuma suna gudanar da harkokinsu a garuruwan Lafia da Karu, bi da bi.
Gwamnan ya gode musu bisa ziyarar da suka kawo tare da ci gaba da ba gwamnatin sa goyon baya.
Ya kuma yaba musu bisa yadda su ka nuna hazaƙarsu ta kasuwanci a jihar da kuma yadda su ke zaune lafiya da masu masaukin su.
Ya buƙace su da su zauna da kowa lafiya a kowane yanki na jihar.
Gwamna Sule ya kuma buƙace su da su tabbatar sun yi rajistar katin zaɓe na dindindin domin kaɗa ƙuri’a a babban zaɓe mai zuwa.