
Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya hana karuwanci da kuma gidajen rawa a Fatakwal, babban birnin jihar.
Gwamnan ya bada umarnin ne a saƙon shi na sabuwar shekara a jiya Asabar, inda ya sanar da hana gidajen rawa, cinikin dare da kuma karuwanci a bakin titi, musamman a kan titin Abacha da sauran gurare, musamman ma a yankin Casablanca.
“A cewa Wike, “wannan zai daƙile illar waɗannan munanan halaye a kan tarbiyar yara masu tasowa.”
Wike ya kuma ce za a kafa wata runduna ta 5saro domin aiwarar da dokar, inda ya umarci jami’an tsaro a jihar da su kama da kuma kai kotu, duk wanda a ka samu ya karya dokar a jihar.
Sai dai kuma, yayin da saura ƙasa da shekaru biyu gwamnan ya sauka da ga mulki, ba a san ko tsawon yaushe dokar za ta kai ba.