Home Labarai Gwamnati na ƙoƙarin shawo kan matsalar mai — Minista

Gwamnati na ƙoƙarin shawo kan matsalar mai — Minista

0
Gwamnati na ƙoƙarin shawo kan matsalar mai — Minista

Gwamnatin Tarayya ta ce ta mayar da hankali ne wajen ganin ta shawo kan matsalar karancin man fetur da layikan mai a ƙasar.

Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a yayin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya duba wasu gidajen mai a babban birnin tarayya, FCT, ciki har da gidajen mai na Conoil da TotalEnergies a yankin tsakiyar birnin.

“Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa dole ne mu tabbatar da cewa yanayin samar da mai ya daidaita cikin sauri. Kuma don haka dole ne in tabbatar da cewa mu na kokarin magance wannan matsala.

“An yi abubuwa da yawa. Kowa na bada gudunmawa kamar su Kamfanin NNPC, Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA), da masu ruwa da tsaki a harkar samar da kayayyaki sun taru domin ganin an shawo kan matsalar.

“Wannan ba lokacin da za mu raba laifi ba ne domin abu mafi muhimmanci shi ne an shawo kan matsalar, kuma za ka ga yanzu layukan sun fara raguwa, akalla a babban birnin tarayya Abuja. Za mu zagaya don tabbatar da sun bace. ” in ji shi.