
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta share wa ƴan Nijeriya hawayensu bisa manya-manyan aiyukan ci gaba da ta gudanar.
Buhari ya bayyana haka ne a yayin buɗe taron bibiyar ƙwazon ayyuka na ministoci domin yin duba a kan cimma nasarar aiwatar da ƙudirori 9 na gwamnatinsa.
A jawabin buɗe taron, Buhari ya lissafa irin gagaruman nasarorin da ya samu a bangaren noma, tattalin arziki, gine-gine , tsaro, lafiya, yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.
Buhari ya shaida hakan ne ga wadanda su ka halarci taron, da su ka haɗa da tsohon shugaban kasar Kenya da ya bar mulki kwanan nan, Uhuru Kenyatta.