
Daga Hassan Y.A. Malik
Gwamnatin Tarayya a yau Lahadi,ta saki sunayen barayin gwamnati mutum 23 wanda cikinsu har da tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da kuma sanatocin jam’iyyar PDP guda 3.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya fitar da wannan sanarwa a jihar Legas, inda sanarwar ta jaddada cewa wannan sabon jerin sunaye da ma wanda gwamnati ta fitar a baya sunaye ne da sai da gwamnati ta tsaya ta tantance tare da tabbatar da samun mutanen da ta fitar da sunayensu da hannu dumu-dumu cikin yin wa-ka-ci-ka-tashi da dukiyar kasa.
Sanarwar na dauke da sa hannun mai bawa ministan yada labarai shawara, Mista Segun Adeyemi.
Ga sabon jerin sunayen wadanda gwamnati ta tabbatar sun yi wa arzikin kasa dibar karan mahaukaciya: