Home Labarai Gwamnati ta yi karin bayanin an saki dukkan ‘yan matan Dapchi

Gwamnati ta yi karin bayanin an saki dukkan ‘yan matan Dapchi

0
Gwamnati ta yi karin bayanin an saki dukkan ‘yan matan Dapchi

Adadin ‘yan matan dapchi da aka sace, wadan da aka sake su a ranar Laraba ya karu zuwa 101 daga 76. Jami’an tsaro sun kattaba sunayen dukkan ‘yan matan da suka samu kubuta daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram, acewar Lai Mohammed.

Da farko dai Minsitan yada labarai Lai Mohammed yace an saki ‘yan mata 76 da sanyin safiyar ranar Laraba, inda yace adadin zai karu na daliban nan ba da jimawa ba, a yayin da ake ta kokarin ganin an kattaba sunayen daliban da aka sako.

Haka kuma, a wata sabuwar sanarwa da Ministan ya fitar, tace daliban da aka saki adadinsu ya karu daga 76 zuwa 101.

Acewar  ministan, sakin ‘yan matan makarantar Dapchi din, yana daga cikin umarnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari  ya bayar ne ga jami’an tsaron da su yi dukkan abinda zasu iya domin su tabbatar da cewar an saki wadannan ‘yan mata da aka sace a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Ministan ya kara da cewar an saki ‘yan matan ne da misalin karfe 3 na asubah, ta hanyar taimakon wasu da suka taimaka wajen ganin an sako wadannan ‘yan mata cikin koshin lafiya ba tare da an cutar  da su ba.

“Domin tabbatar da cewar an saki matan lami lafiya, Gwamnati ta bayar da umarnin janye dukkan jami’an tsaro daga yankin dan kada a samu matsala ta kai musu farmaki ko tunanin wani abu da ka iya kawo tsaiko kan batun”

“A lokacin da aka dawo da ‘yan matan, an dakatar da dukkan wasu jami’an tsaro daga yankin, domin samun hucewar ‘yan kungiyar ta Boko Haram lami lafiya ba tare da wata matsala ba”

Bayan haka kuma, tawagar Gwamnatin tarayya da ta hada da Ministan yada labarai da ministan harkokin cikin gida da karamar ministar harkokin waje suna kan hanyars ta zuwa Maiduguri domin saduwa da ‘yan matan da aka sako yau da safe.