Home Labarai Gwamnati zata sanya kafar wando daya da Sarkin Kano kan zargin da ya yiwa Ministoci a Amurka

Gwamnati zata sanya kafar wando daya da Sarkin Kano kan zargin da ya yiwa Ministoci a Amurka

0
Gwamnati zata sanya kafar wando daya da Sarkin Kano kan zargin da ya yiwa Ministoci a Amurka

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin da mai martaba Sarkin kano, Muhammadu Sunusi II ya yiwa Ministocin Gwamnatin tarayya wanda aka gayyace su taro Amurka domin tattaunawa kan yadda ‘yan kasuwar Amurka zasu zuba jari a Najeriya.

Taron da ya gudana a ranar 19 ga watan Afrilun nan a birnin Washington dake gundumar kwalambiya,inda mai Martaba Sarkin ya zargi ministocin da kin halartar taron da suka je Amurka dominsa.

Mai Martaba Sarkin Kano, wanda yayi magana da masu aiko da labarai bayan kammala zaman farko da manyan ‘yan kasuwar Amurka masu zuba jari, ya bayyana abinda Ministocin suka yi na kin halartar taron da suka je kasar Amurka dominsa, wanda aka tsara zasu yi jawaban da zasu janyo hankulan ”yan kasuwar domin su zuba jari a Najeriya, amma ministocin suka bige da yawon gantali.

Taron wanda aka yiwa take da cewar “Najeriya kasar da ta budewa ‘yan kasuwa kofa” an tsara taron inda masana daga Najeriya da kuma kasar Amurka zasu tattauna domin barinilimi ga dukkan bangarori guda biyu na Gwamnatin Najeriya da kuma na manyan ‘yan kasuwar Amurka da zasu iya zuba jari a Najeriya.

Haka kuma, a wata sanarwa da ya fitar a birni Landan a ranar Litinin, Ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, yace mafiya  yawancin ministocin da aka tsara zasu yi jawabi a wajen taron, galibinsu basu ma iso birnin Washington ba balle a zarge su da kin halartar taron, zargin cewar Ministocin sun karbi alawus din  zuwa Amurka sun kama gabansu bai taso ba.

Ya karada cewar”Daga cikin wadan da aka tsara zasu yi magana a wajen taron, akwai Ministan ayyukan gona da na Ayyuka da gidaje da kuma ministan kasafin kudi da tsare tsare, amma duk da akwai sunayensu zasu yi jawabi, basu ma samu takardar gayyatar taron ba”.

Yace ministar kudi, wadda take birnin Washington lokacin da ake taron, ya bayyana cewar abinda ya kaita Amurka daban, ba wai wajen taron taje ba.