
Gwamnatin jihar Adamawa ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu cikin gaggawa a jihar sakamakon barkewar cutar kyanda.
Umurnin, wanda aka bayar a yau Litinin, na da nufin rage yaduwar cutar tare da baiwa hukumar kula da lafiya matakin farko ta jiha (PHCDA) damar yi wa masu shekaru masu rauni allurar rigakafi.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi da ci gaban jama’a, Aisha Umar, ma’aikatar ta mayar da ranar komawa makaranta zuwa ranar litinin 13 ga watan Mayu 2024.
Sanarwar ta kuma umarci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su bi wannan umarni.
Tuni dai bullar cutar ta lakume rayukan yara 42 a jihar, sai dai gwamnatin ta ce tana daukar matakan da suka dace domin dakile cutar da kuma hana samun asarar rayuka.