Home Labarai Gwamnatin Anambra ta rushe maɓoyar masu garkuwa da mutane

Gwamnatin Anambra ta rushe maɓoyar masu garkuwa da mutane

0
Gwamnatin Anambra ta rushe maɓoyar masu garkuwa da mutane

 

 

 

Gwamnatin Jihar Anambra ta rushe wani gini da ake zargin ana amfani da shi a matsayin maɓoyar gungun masu garkuwa da mutane a ƙauyen Okpuno-Ifite, Oba, Ƙaramar Hukumar Idemili ta Kudu a Anambra.

An gudanar da rushe ginin ne yayin wani samame da rundunar haɗin gwiwa ta vigilante, ‘yan sanda, sojojin ƙasa da na ruwa da kuma jami’an ƴan sandan farin kaya a ranar Juma’a.

Ginin, tsohon gida ne mai ɗakuna 4 da ke tsakiyar jama’a kuma kewaye da gidaje.

Wasu daga cikin abubuwan da aka samu a gidan sun haɗa da bindigar ƙirar gida, wurin bauta, layu da magungunan tsari na gargajiya, yanar wiwi, da dai sauran kayayyakin laifi.

Da ya ke tsokaci game da rushe ginin, Gwamna Chukwuma Soludo ya ce samamen da s ka kai a baya bayan nan ne ya kai ga ceto wani babban malamin addinin kirista na Cocin Katolika tare da ƙwato motarsa ​​da ma wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su da ke tsare.

Soludo ya yaba da kokarin da rundunar tsaro ta hadin gwiwa ke yi, yana mai cewa aikin rusau ɗin zai zama izina ga sauran masu aikata laifuka.